Jiga jigai a jam’iyyar PDP da suka hada da Farfesa Jerry Gana da Farfesa Rufai Alkali da Farfesa Tunde Adeniran da kuma Dakta Junaidu Muhammad su koma sabuwar jam’iyyar SDP ta Cif Olu Falae.

A cewarsu sun sauya shekar ne domin karfafa demokaradiyyar Najeriya, domin jam’iyyar ta zama ta uku mafi girma bayan jam’iyyun APC da PDP, domin samarwa da ‘yan Najeriya madogara a zaben 2019.

Sabuwar jam’iyyar SDP dai na karkashin Shugabancin Cif Olu Falae, tsohon Sakataren Gwamnatin tarayyar Najeriya.

Jam’iyyar SDP din ta bayyana cewar, ita jam’iyya ce ta dukkan ‘yan Najeriya a cewar Farfesa Jerry Gana bayan sun gama ganawa da kwamitin amintattun jam’iyyar.

LEAVE A REPLY