Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa jam’iyyar adawa ta PDP wankin babban bargo, inda ya bayyana cewar, a tsawon shekaru 16 da PDP, ta yi tana jan ragamar Gwamnatin Najeriya, ta sace dalar Amurka biliyan 500 na kudin mai da Gwamnati ta samu.

SHugaba Buhari yana magana ne a wani taron masu ruwa da tsakani na jam’iyyar APC da akai a babban dakin taro na Banquet dake fadar Shugaban kasa a Villa, a ranar litinin. Shugaba Buhari yace, sauran kiris da Najeriya ta durkushe sabida muguwar satar da ‘yan PDP suka yi.

“Abu ne mai sauki ‘yan Najeriya su mance da batun zambar da ake i da sunan bayar da tallafin shigo da man fetur, da yadda ake karkata akalar makamai, da wawushe asusun tara rarar kudin man fetur na Najeriya, ga kin biyan ‘yan kwangila da ake yi na hakkokinsu. Ga kuma kin saka kudin gwamnati a fannin gine ginen hanyoyi da aikin jirgin kasa da batun lantarki, bayan kuma irin dumbin kudaden da aka samu daga cinikin man fetur da gas na sama da biliyan 500 na dalar Amurka”

Haka kuma, Shugaban jam’iyyar APC na kasa John Oyegun, yayi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar ta APC da su mance dukkan wani bambance bambance dake tsakaninsu, su kuma shiryawa zaben jihohin Osun da kuma Ekiti da za’a yi nan gaba.

“Akwai sabani da rashin fahimtar juna mai yawa a tsariin siyasar Demokaradiyya a ko ina, amma ba zamu taba bari irin wadannan sabani da rashin fahimta su janyo mana koma baya a jam’iyyarmu ba, babban burinmu shi ne samaun nasarar dukkan wasu zabubbuka da zamu shiga, domin kafa Gwamnati a dukkan matakai”

“A sabida haka, ina mai jaddada goyon bayana ga kwamitin sasanta ‘yan jam’iyyar da basa ga miciji da juna wanda Asiwaju yake Shugabanta, wanda Shugaban kasa ne da kansa ya nada shi, a sabida haka nake kira da a baiwa wannan  kwamiti dukkan goyon bayan da ya dace da shi”

“Samun Nasarar wannan kwamiti, shi ne tabbatar dorewar samun nasarar wannan jam’iyya a sauran zabubbukan dake tafe nan gaba”

“Duk da cewar akwai kalubale da yawa a gabanmu, amma wannan ba zai sare mana guiwa ba wajen yin aiki tukuru domin samun nasarar wannan jam’iyya da kuma Gwamnatin da muka kafa.”

LEAVE A REPLY