Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta lashe zaben cike gurbi da aka yi na dan majalisar dokokin jihar Taraba mai wakiltar karamar hukumar Takum 1 a jihar da aka gudanar a jiya Asabar.

Ajiya Samson Ajiya wanda ya yiwa jam’iyyar PDP takarar dan majalisar shi ne ya samu galaba akan dan takarar jam’iyyar APC Antem Ansho da kuri’u 14,337 yayin da wanda aka kayar ya samu kuri’u 10,725.

LEAVE A REPLY