Jam’iyyar PDP a jihar Delta ta lashe zabukan kananan hukumomi da aka bayyana sakamakonsa  ranar Lahadi a Asaba a jihar ta Delta. PDP ta cinye 23 daga cikin kananan hukumomi 25 din da aka yi zabe.

Shugaban hukumar zaben jihar Mista Mike Ogbudu ne ya bayyana hakan a Asaba lokacin da yake bayar da sakamakon zabe na karshe da aka gudanar a jihar.

Yace jam’iyyar PDP taci nasarar lashe zaben kananan hukumomi 23 na jihar. Sannan ya kara da cewar, ragowar kananan hukumomi guda biyu da ba’a yi zabe ba,an dage zaben sai wani lokaci nan gaba.

Yace za’a gudanar da zaben kananan hukumomin Ethipo ta Gabas da kuma Ughelli ta Arewa a ranar 9 ga watan Janairun 2018.

Sai dai SHugaban jam’iyyar APC na jihar Mista Jones Erue yayi watsi da wannan sakamakon zabe, yace ba’a bi ka’idodin da suka dace ba wajen aiwatar da wannan zaben, a cewarsa suna tattaunawa domin daukar mataki na gaba.

 

LEAVE A REPLY