Balarabe Musa

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna a zaminin mulkin jamhuriya ta biyu, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya tofa albarkacin bakinsa kan ficewar Shugaban majalisar  dattawa Bukola Saraki daga cikin jam’iyyar APC zuwa PDP.

Balarabe Musa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidansa dake Kaduna, inda yace, ficewar Saraki daga cikin jam’iyyar APC babban koma baya ne ga jam’iyyar ta APC, hakan kuma alamu ne dake nuna cewar jam’iyyar na cikin gagarumar matsala.

Yace babu ko shakka wannan ficewa ta Saraki daga APCzata shafi nasarar Shugaba Buhari da jam’iyyar APC a zaben shekarar 2019 dake tafe.

Idan za’a iya tunawa aranar Talata ne dai Shugaban majalisar dattawa ta kasa Bukola Saraki ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.

 

LEAVE A REPLY