Hassan Y.A. Malik

Daliban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse, jihar Jigawa, FUD, 54 ne suka samu kammala jami’ar da digiri mai daraja ta daya.

Shugabar jami’ar, Farfesa Fatima Batul-Muktar ce ta bayyana hakan a jiya Litinin a birnin Dutse, a wani shiri na bikin yaye daliban.

Farfesa Batul, ta bayyana cewa dalibai 427 jami’ar ta yaye a bangarorin ilimai daban-daban a bana, kuma a cikinsu, guda 54 sun kammala da digiri mai daraja ta daya, 223 kuma da digiri mai daraja ta biyu, sai 149 kuma da digiri mai daraja ta uku, inda dalibi 1 tilo ya gama da digiri mai darajar da kyar na sha.

Shugabar ta ci gaba da cewa, tun bayan bude makarantar a shekarar 2011, jami’ar ta ci gaba da samun nasarori ta bangaren harkokin koyo da koyarwa da ma samar da gine-ginen azuzuwa, dakunan karatu da ofisoshin ma’aikata da kuma kirkirar sababbin tsangayoyi.

“Mun fara ne da tsangayoyi 5 kacal a shekarar karatu ta 2011/2012, amma zuwa yanzu makaratar na da tsangayu 19 kuma adadin dalibai ya tashi daga 202 a sheakarar budewa zuwa 5,963 a halin yanzu.”

Farfesa Batul ta ci gaba da cewa, yana cikin tsare-tsaren da hukumar jami’ar ke yi na bude wata sabuwar tsangaya ta ilimin gudanarwar rayuwar dan adam da dabi’unsa, wanda za a fara karatu a tsangayar a watan Satumba mai zuwa.

Zuwa sheakarar 2019 kuma, jami’ar za ta bude tsangayar karantar da ilimi matakin farko don ta bada nata gudunmawar wajen horar da malamai a kasar nan.

LEAVE A REPLY