Daga Hassan Y.A. Malik

Mataimakin shugaban jami’ar Bayero Kano, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, a jiya Talata ya bayyana shirye-shiryen da jami’ar ke yi na bude gidan talabijin da radiyo a cikin jami’ar.

Farfesa Yahuza ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye dalibai karo na 34 da jami’ar ta gudanar a jiya, inda ya bayyana cewa, jami’ar Bayero za ta yi kafada da kafada da takwararta ta jiha Legas a matsayin jami’o’i biyu a fadin kasar nan da ke da gidajen radio da talabijin mallakin kansu.

Ya ci gaba da cewa, tuni dai aikin dasa kayan aiki da jami’a ta yi odarsu daga waje ya yi nisa, kuma da zarar jami’ar ta samu sahalewar yada shirye-shiyenta daga hukumar sanya idanu akan harkokin yada labarai, NBC.

Tuni dai dama jami’ar na da irin wannan sahalewa ta bangaren yada shirye-shiryenta ta radiyo a cewar Shehin Malami Yahuza Bello.

LEAVE A REPLY