Jami'ar ATBU

Daga Hassan Y.A. Malik

Hukumomi a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ake kira a takaice da ATBU Bauchi sun bayyana korar wani shehin malami da ke aiki a makarantar tare dawani babban lakcara sakamakon samunsu da karya dokar aikin makarantar.

Hukumar gudanarwar jami’ar ce ta amince da korar ta Farfesa Aminu Ahmad Rufa’i na sashen koyar da ilimin yadda jikin mutum ke aiki (Human Anatomy) da ke tsangayar kimiyyar likitanci ta jami’ar da kuma wani Dakta Idris Isyaku Abdullahi na sashen koyar da nazarin lissafi da sha’anin kudi (Accounting and Finance) da ke tsangayar kimiyyar gudanarwa.

Korar na malaman biyu na cikin wata sanarwa ta hanyar takarda da makarantar ta fitar mai lamba: ATBU/REG/ACAD/PER/01348 mai dauke da kwanan watan 27 ga watan Afrilu, 2018.

Takardar na dauke da sa hannun mataimakin rajistara na jami’ar mai kula da harkokin manyan ma’aikata, Aminu Yakubu Gambo tare da bayanin shawarwarin da kwamitin ladabtarwa ta jami’ar ta bayar.

ATBU ta kama Farfesa Aminu Ahmad Rufa’i ne da laifin hada ayyuka na din-din-din guda biyu kuma yana karbar albashinsu a karshen kowane wata, inda shi kuma Dakta Idris Isyaku Abdullahi aka same shi da aikata laifin shirya sharri, kage, kazafi da bata sunan jami’ar ta ATBU.

Hukumar ATBU ta bayyana wannan kora da ta ayyana akan wadannan ma’aikata nata biyu da ya fara nan take, tare kuma da jan hankalinsu da su gaggauta mika duk wani mallaki na jami’ar da ke hannunsa ga hukumomin da suka dace.

LEAVE A REPLY