Hukumar tsaron sirri ta farin kaya a Najeriyar DSS, cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da kwanan watan 21 ga watan Yunin 2018 ta ce ta yi nasarar kame kwamandojin na kungiyar IS a yammacin Afrika ne ranar 5 ga watan Mayu a wajen Abuja babban birnin Kasar.

Sanarwar ta nuna cewa Kwamandojin na IS a Yammacin Afrika kungiyar da aka fi sani da ISWA, na shirin hada hannu da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a Najeriyar wajen kai hare-hare kan mutanen da basu-ji-ba basu-gani-ba.

Haka zalika hukumar tsaron ta DSS ta ce ta kuma kame wasu mambobin kungiyar boko Haram 4 ciki har da kwararru ta fuskar hada bama-bamai.

Kamen dai na zuwa ne bayan wani rahoton jaridar Birtaniya da ya yi nuni da cewa, akwai tarin mayakan IS da ke neman damar shiga Najeriyar don kai hare-haren ta’addanci bayan fatattakarsu daga kasashen Iraqi da Syria.

Najeriyar wadda ke fuskantar matsalar tsaro, yanzu haka hare-haren ta’addancin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar ya hallaka fiye da mutane dubu 20 daga shekarar 2009 zuwa yanzu.

HA.RFI.FR

LEAVE A REPLY