Tsohon Gwamnan jihar Binuwai Suswam

Tsohon Gwamnan jihar Binuwai, Gebriel Suswam ya fada komar hukumar tsaron farin kaya ta SSS bisa zarginsa da ake yi da hannu wajen tashe tashen hankula a jihar da suke da nasaba da kashe kashen mutane da ake yi babu gaira babu dalili.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewar an kame Suswam ne, bayan da Gwamnan jihar Binuwai mai ci Samuel Ortom ya rubutawa hukumar kokensa kan tsohon Gwamnan.

A cewar wata majiya daga fadar Gwamnatin jihar Binuwai, Gwamna Ortom ya zargi tsohon Gwamnan Suswam da ynkurin mayar da jihar ta Binuwai zuwa wani fagen daga da zai kasance cikin tashin hankali a koda yaushe.

 

LEAVE A REPLY