Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Uche Secondus

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana ra’ayinta kan abinda jami’an tsaro suka yi na tarewa wasu daga cikin ‘yan majalisa hanyar shiga harabar majalisar a safyar yau Talata.

PDP ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter, inda ta kira abinda cewar “Abin tur ne da Allah wadai kan yadda ake son taka doka domin biyan bukatarsu”

“Wannan abinda jami’an tsaro suka yi ba karamar danja bace ga demokaradiyyar Najeriya, sun aikata mummunan laifi” A cewar jam’iyyar adawa ta PDP.

LEAVE A REPLY