Gwamnan Ekiti Ayo Fayose

Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya gargadi jami’an tsaro da hukumar zabe ta kasa INEC da su guji duk wani yunkuri da zai kai ga murde zaben Gwamnan jihar Ekiti domin taimakawa jam’iyyar APC mai mulki samun nasarar zaben.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen gangamin da jam’iyyar ta yi a ranar Alhamis domin mika tutar jam’iyyar PDP ga dan takarar Gwamnan jihar Farfesa Kolafo wandasi ne mataimakin Gwamnan jihar.

Za’a gudanar da zaben Gwamnan jihar Ekiti ne a mako mai zuwa 14 ga wannan watan. Manyan ‘yan takarar Gwamnan jihar dai guda biyu ne, tsohon Minista Kayode Fayemi wanda ya taba yin Gwamnan jihar da kuma shi mataimakin Gwamnan na yanzu.

Akwai dai zazzafar hamayya tsakanin jam’iyyun APC da PDP akan wannan zabe, wanda shi ne ake ganin zai iya zama zakaran gwajin dafin zaben shekarar 2019 dake tafe.

LEAVE A REPLY