Dakta Yunusa Adamu Dangwani

Daga karshe dai jami’an tsaron SSS sun saki babban na hannun daman Kwankwaso kuma jigo a cikin tafiyar Kwankwasiyya, Dakta Yunusa Dangwani bayan da ya shafe kwanaki 84 a tsare a hannun jami’an.

Jami’an tsaro sun kama Dakta Dangwani ne a ranar 21 ga watan Maris a filin sauka da tashin jiragen saman Malam Aminu Kano akkan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya domin yin Umara.

Dakta Yunusa Dangwani dai shi ne tsohon Shugaban ma’aikatan tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

An kama Dakta Dangwani ne sakamakon zargin sa da ake yi da sanya wani mutum Captain Abdullahi da ya yada wani sakon tes na waya, inda yake yin barazana ga zaman lafiya da kuma tsaro a jihar Kano, sakon da aka ce yaje har wayar mai dakin gwamnan Kano.

 

LEAVE A REPLY