Daga Hassan Y.A. Malik

Hukumar tsaron kare farar hula al’umma ta sibil difens reshen jihar Jigawa ta yi nasarar kama wasu mutane uku bisa zargin barayin kayayyakin wutar lantarki ne.

Mai Magana da yawun hukumar Adamu Shehu ya bayyana haka ga manema labarai anan Dutse,inda ya ce an kama wadanda ake zargin ne a karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa da karamar hukumar Baure ta jihar Katsina.

Ya ce kayayyakin mallakar gwamnatin jihar Jigawa ne da kuma kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO.
Adamu Shehu ya kara da cewa an yi Kaman ne bisa rahotan da hukumar ta samu daga sashen ayyuka na karamar hukumar Babura.

Malam Adamu ya ce masu laifin sun amsa laifinsu,inda suka sayar da kayayyakin akan kudi naira dubu tara da dari biyar da kuma dubu bakwai da dari biyar.

LEAVE A REPLY