Shugaban Jimhuriyyar Nijar Mohammdou Isoufou
Daga Saadatu Baba Ahmed
A ci gaba da ziyarar Mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi II ya ke a kasar Jamhuriyar Nijar don amsa gayyatar taron gyara zamantakewa a kasar wanda ya kunshi tattaunawa akan matsalolin auratayya da inganta ilimi da kuma kira ga masu hali da su tallafawa harkokin ilimi.
Taron dai na Musamman ne da Ma’aikatar Kyautata al’adu da Cigaban rayuwar al’umma ta Jamhuriyar  Niger ta Shirya karkashin daukar bakuncin Mai girma Shugaban kasar Niger, El Hadj Issoufou Mahamadou.
Taken taron: Addinin Musulunci da kyautata zamantakewar Al’umma, Wanda Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya jagoranci Malamai na Nigeria don aiwatar da kundin tsarin a Kasar Niger.
Dubban ‘yan kasar Nijar da suka halacci taron yayin gabatar da mukalar mai martaba Sarkin a National conference Centre sun yi ta tafi da jinjina bisa muhimman batututuwan da sarkin ya tattauna a kansu a gaban Shugaban Kasa Issofou Muhamdou da prime Minister da Ministan cikin gida  da Ministan al’adu tare Kakakin majalisar kasar da sauran Ministoci da Sultan na Damagaram da Sarkin Konni da Sarkin Tahoua da kuma sauran Sarakunan Niger da Majalisar malamai ta kasar Shugaban Kasa.

LEAVE A REPLY