A ranar Asabar ne jam’iyyar PDP a jihar Kaduna ta tantance Malam Salihu Sagir Takai domin neman kujerar Gwamnan jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewar Sanata Kwankwaso yayi duk yadda zai yi akan ya lallabi Takai ya karbi takarar Sanatan Kano ta kudu amma abin yaci tura.

Malam Salihu Sagir Takai yaki yadda da tayin Kwankwaso na yin takarar kurjarar dan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta kudu Domin ya bar masa kujerar Gwamna dan ya nada dan Kwankwasiyya.

Bayanai sun nuna cewar bayan da Takai yaki yadda da tayin Kwankwaso na yin takarar Sanata, Kwankwaso ya fito da sirikinsa Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takararsa daga bangaren Kwankwasiyya.

LEAVE A REPLY