Daga Hassan Abdulmalik

Tun bayan da Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bankada asirin abinda kowane sanatan Nijeriya ke tafiya da shi gida a kowane wata, a matsayin kudi Naira da gugar Naira har miliyan 13.5, banda albashinsa na Naira dubu 750, al’umma ke ta bayyana ra’ayoyinsu kan rashin fahimtar me kudin gudanarwar ma ke nufi.

Kudin gudanarwar Sanatoci dai a binciken mun gano cewa kudade ne na alawus da ake warewa kowane sanatan Nijeriya don gudanar abubuwa da suka shafi gudanar da aikinsa ga kasa a matsayin sanatan Nijeriya.

Bisa ka’ida, kowane sanata sai ya dawo da risitin yadda ya kashe wadannan kudade, ko kuma ya dawo da rararsu:

Ga yadda fasalin kudin gudanarwa take:

Alawus na jarida….. Naira miliyan 1.2 a wata

Alawus na sutura….. Naira dubu dari 620

Alawus na shakatawa…………….. Naira dubu dari 250

Alawus na muhalli….. Naira miliyan 4.97

Alawus na wutan lantarki/ruwa da sauransu… Naira dubu dari 830

Alawus na barorin gida….. Naira miliyan 1.86

Alawus na nishadi………….. Naira dubu dari 830

Alawus na hadimi na musamman…. Naira dubu dari 620

Alawus na kula da abin hawa…. Naira miliyan 1.86

Alawus na hutu…………… Naira dubu dari 250

 

Jimilan kudi = Naira miliyan 13.58 a kowane wata
Kudin gudanar kowane sanatan Nijeriya na shekara guda ya kama = Naira miliyan 162.96.

 

Albashin Sanata na wata = Naira dubu 750.

Albashin sanata na shekara ya tashi Naira miliyan 9 daidai.

Haka kuma. ana bawa kowane sanata Naira miliyan 200 a shekara don gudanar da ayyuka ga mazabarsa.

A takaice dai, sanata na daukar:

Naira miliyan 9 a shekara a matsayin albashi

Naira miliyan 163 a shekara a matsayin kudaden gudanarwa

Naira miliyan 200 a matsayin kudaden ayyuka wa mazabu

 

Jimilla ya kama:
Naira miliyan 372 a shekara

 

Banda wannan kuma, ana bawa sanatan Nijeriya:

Naira miliyan 7.43 a matsayin giratuti in zai bar majalisa.

Naira miliyan 7.45 a matsayin alawus din kayan daki.

Naira miliyan 9.94 a matsayin alawus din sayen mota.

Wannan ya kama Naira miliyan 24.82

LEAVE A REPLY