Sanata Binta Masi Garba

Sanata mai wakiltar Arewacin jihar Adamawa a majalisar dattawan Najeriya, Binta Masi Garba, ta bayyana yadda mahaifinta ya kusan halakata a saboda ta bar  Musulunci zuwa Kiristanci.

Binta Masi Garba na magana ne lokacin da aka shirya mata adduar nuna godiya ga Allah lokacin bikin cikarta shekaru 50 a duniya, a cocin Chapel Praise International dake birnin Yola a ranar Lahadin da ta gabata.

“Na mika dukkan lamuran rayuwata zuwa ga Almasihu a lokacin da nake ‘yar makaranta, mahaifina ya fusata, dan haka ya kone komai nawa, saboda na zabi addinin kiristanci akan na Musulunci”

“Na sha bakar wahala a wajen iyayena, saboda kiristanci da na koma. Ba dan Yesu Almasihu ba, da ni ba komai bace” A cewar Sanata Binta Garba.

 

LEAVE A REPLY