Kasar Israela ta baiwa baki ‘yan Afurka mazauna kasar watanni biyu da su fice su san inda dare yayi musu ko kuma su fuskanci fushin hukumomin kasar.

Gwamnatin Firaministan kasar Benjamin Netanyahu, ta baiwa bakin zabin karbar dalar Amurka 3,500 tare da tikitin komawa gida, ko kuma wanda duk yaki yadda da wannan tayi ya kwashi kashinsa a hannu.

Mafiya yawan wanda wannan abin ya shafa sun fito daga kasashen Eritiriya da kuma Sudan ta kudu.

Akalla akwai baki ‘yan AFurka da suke zaune a kasar sama da mutum 37,000 wanda suke ganin kasar ta Yahudu a matsayin tudun mun tsira daga halin tsananin rayuwa da suke fama da shi.

Gwamnatin tace tana samun matsin lamba akan ta sallami baki ‘yan Afurka zuwa gida domin cigaba da rayuwarsu a can.

Gwamnatin tace, mutanan da suke zaune a kasar da yawansu neman aikin yi suke maimakon zaman mafaka da suka shigo kasar dominsa.

Amma sai dai akwai wasu gungun ‘yan Nazi da aka fi sani da Rabbi da suke ganin bai kamata Gwamnatin kasar ta sallami bakin hauren ba, a cewarsu kamata yayi Israela ta nuna musu kauna da kuma karamci.

Gwamnatin dai ta bayar da wannan sanarwa ne a shafukan intanet mallakar Gwamnatin, inda tace tana neman ma’aikatan da zasu yi mata dawainiyar sallamar bakin hauren.

 

LEAVE A REPLY