Isa Yuguda

Tsohon Gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya kaddamar da takarar Sanatan Bauchi ta kudu a majalisar dattawan Najeriya.

Za a gudanar da zaben cike gurbin kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Bauchi ta kudu, tun bayan rasuwar Sanata Ali Wakili wanda Allah ya yiwa rasuwa a 17 ga watan Maris din da ya gabata.

Ko a zaben shekarar 2015 da ya gabata, Isa Yuguda yana matsayin Gwamnan Bauchi a karkashin jam’iyyar PDP ya nemi kujerar Sanatan Bauchi ta kudu, amma ya sha kaye a hannun Ali Wakili na jam’iyyar APC, a wani abu da ake ganin jam’iyyar APC ta yi mamaye a jihohin Arewacin Najeriya.

Yuguda wanda yanzu ya koma sabuwar jam’iyyar GPN, ya bayyanawa ‘yan jarida a garin Bauchi cewar a yanzu ma zai sake gwada sa’arsa ta neman kujerar Sanatan Bauchi ta kudu a majalisar dattawan Najeriya.

 

LEAVE A REPLY