Bala Muhammad

Dr. Bala Muhammad na sashin sadarwa dake jami’ar Bayero a Kano, ya zargi Inyamurai da yaduwar miyagun kwayoyin da ake sha don a bugu a Arewacin Najeriya.

Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gabatar da wata mukala a wani taron Matasa da aka yi a Kano, wanda Gidauniyar hamisu Magaji ta shirya a gidan tunawa da marigayi Malam Aminu Kano dake Mumbayya.

A yayin da yake gabatar da mukalar akan “matasa da shaye shaye da ayyukan ta’addanci da kuma rashin tsaro”Malamin ya zargin manyan dilolin magunguna na kabilar Ibo dake kasuwannin jihar Kano da yada wadannan miyagun kwayoyi ga matasan Arewacin Najeriya.

A jawabin nasa, yace a yankin Kudu maso Gabas inda nan ne yankin Inyamurai, babu matsalar shaye shayen miyagun kwayoyi kamar yadda ake kuka da ita a Arewacin Najeriya.

“Inyamurai sune suke samar da dukkan magungunan da ake sha a bugu, binciken da muka yi ya tabbatar mana da haka”

“Shaye shayen da ake yi yanzu ya wuce wiwi ko giya ko hodar Iblis da aka sani, yanzu abin ya wuce nan, magungunan tari da ake kara musu sindarai su matasa suke sha domin su bugu”

“An sha kama inyamurai a lokuta da dama akan batun shigo da miyagun kwayoyi da magungunan da ake sh don a bugu a kasuwannin jihar Kano dama sauran garuruwan Arewacin Najeriya”

“Me yasa ba zasu dauki wadannan miyagun kwayoyi zuwa yaninsu na Inyamurai ba suka kawo mana su? Wannan yake nuna cewar akwai wata nufaka da mugun nufi a tare da su ga al’ummar Arewacin Najeriya” AcewarBala Muhammad.

 

LEAVE A REPLY