Gwamnan Kogi Yahya Bello

Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewar zata gurfanar da Gwamnan jihar Kogi Yahya Bello sabida yayi rajistar katin zabe sau biyu.

“Hukumar zaben tace batun yin katin zabe sau biyu da Gwamnan yayi, ba zai tafi a banza ba, dole ya fuskanci hukunci, amma sai dai ba zata iya gurfanar da shi yanzu ba sabida yana da rigar kariya da yake da shi a matsayinsa na Gwamna mai ci”

“Gwamnan ya aikata laifin da ya saba da doka, kuma dole ya fuskanci hukunci” a cewar Kwamishinan hukumar zabe ta kasa reshen jihar Kogi Mista James Apam, ya bayyana hakan ne a birnin Lakwaja ranar Alhamis.

A shekarar da ta gabata 23 ga watan Mayu, hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewar yin katin shaidar zabe karo biyu da Gwamnan jihar Kogi Bello yayi a bai dace ba.

LEAVE A REPLY