Shugaban hukumarzabe ta kasa, farfesa Mahmud Yakubu

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta bayyana cewar ta shirya tsaf domin gudanarda zaben cike gurbi a jihohin Katsina da Bauchi da kuma Kuros-Riba.

Hukumar zaben ta shaida cewar a ranar Juma’a zata fadi ranakun da zata aiwatar da zabubbukan cike gurbin ‘yan majalisun tarayya a jihohin.

Shugaban hukumar zaben ta kasa INEC Farfesa Mahmud Yakubu shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da kwamishinonin hukumar na jihohin kasarnan a ranar Laraba a babban birnin tarayya dake Abuja.

Farfesa Yakubu ya bayyana cewar ranakun da za’a bayyana zasu kunshi lokacin da za’a yi zaben cike gurbin ‘yan majalisar  dattawa na jihohi Katsina da Bauchi da kuma dan majalisar wakilai na Lakwaja/Koton Karfe a jihar Kogi da kuma dan majalisar wakilai na Obudu a jihar Kuros-Riba.

 

 

LEAVE A REPLY