Sanata Dino Melaye

Daga Hassan Y.A. Malik

Hukumar Zabe mai zaman kanta, INEC ta saki jadawalin kiranye ga sanata mai wakiltar Kogi ta yamma, Dino Melaye.

A sanarwar da INEC ta fitar a jiya Juma’a wanda sakatariyar hukumar, Misis Augusta Ogakwu ta sanya wa hannu ya bayyana cewa za a fara aikin kiranyen ne a ranar Talata, 27 ga watan Maris, 2018.

Kiranyen zai fara ne da aikawa da sakon tantancewa zuwa ga ofishin hukumar da ke Lokoja, jihar Kogi, sannan zai kare da bayyana sakamakon kiranyen da zai nuna ko Dino zai ci gaba da zama a majalisar dattijai ko kuma zai dawo a ranar 29 ga watan Afrilu, 2018.

INEC ta bayyana cewa tsarin kiranyen da ta fitar ya biyo bayan hukuncin kotun daukaka kara mai zamanta a Abuja da ta fitar a ranar 16 ga watan Maris, 2018, inda kotun ta bawa hukumar ta INEC damar ci gaba da aikin yin kiranyen a matsayin daya daga cikin hakkokinta na dawo da dan majalisa in har bukatatr hakan ta taso daga mazabarsa.

LEAVE A REPLY