Daga Hassan Y.A. Malik

Wata kotun al’adu da ke a garin Ile-Tuntun, Ibadan, babban birnin jihar Oyo ta raba wani aure na shekaru 11 a jiya Talata bayan da ta fahimci rikicin da ke tsajanin ma’auratan, Timisiyu Adegoke da matarsa, Modupe ba zai sulhuntu ba.

Kotun ta raba auren ne bayan da Timisiyu ya tabbatarwa da kotu ta hanyar mika wasu wayoyi hannu guda biyu a matsayin shaida yadda matarsa, Modupe, uwar ‘ya’yansa 2 ke mu’amalar banza da maza a waje.

Timi ya bayyanawa kotu irin yadda ya samu yadda matarsa ke turawa wasu maza hotunanta tumbir ta hanyar kafar yada zumunta ta WhatsApp da kuma yadda hirarta da wasu cikin samarinta ya gudana na yadda suka ji dadin juna a haduwarsu ta baya.

Ita ma Modupe ta bayyana cewa ta gaji da auren sakamakon abinda ta kira rashin imani da Timisiyu ke gwada mata ta hanyar lakada mata uban duka da zarar wani abu komai kashinsa ya shiga tsakaninsu.

Shugaban kotun, Cif Henry Agbaje ya bayyana raba auren bayan abibda ya kira rikicin da ba zai sulhuntu ba tsakanin ma’auratan.

Cif Henry ya ci gaba da cewa, kotu ba ta murna da mace-macen aure, amma in har rikici tsakanin ma’aurata ya kai irin wannan matsayi, to fa abinda ya fi shi ne a raba auren don gudun kar ma’auaratan su tafka aika-aika.

“Bisa wannan dalili ne na raba auren Timisiyu da Modupe bisa sharadin Modupe za ta ci gaba da rike ‘ya’yansu biyu, haka kuma Timisiyu zai dinga bawa Modupe Naira 4,000 a duk watan duniya domin kula da ‘ya’yansu.

LEAVE A REPLY