Daga Yakubu Liman
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Sadiya ta ce tana nan da ranta. Sabanin jita-jitar da ake yadawa a shafukan sada zumunta cewa ta mutu.
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Sadiya Mohammed wacce aka fi sani da Sadiya Gyale ta karyata cewa ta mutu. Domin tana nan da ranta ba kamar yadda ake jita-jitan cewa ta rasu ba.
A wata hira da jaridar Daily Nigerian ta yi da Baballe Hayatu daya daga cikin jarumai a masana’antar, kuma abokin aikin Sadiya, ya karyata jita-jitan. Ya kuma sa hirar da suka yi da ita a waya a safiyar Alhamis din nan.
A hirarsu da ita wanda ya kuma ya sa muka ji a wayarsa, Sadiya na cewa tana nan da ranta, kuma lafiyarta kalu.
 Baballen ya kuma nuna takaicinsa na irin wannan dabi’a na kirkirar labarin cewa wani jarumi ko jaruma ta mutu ba gaira babu dalili.
 Wannan ba shi ne karon farko da ake yadda labarin karya na mutuwar wani jarimi ko jaruma a  masana’antar shirya fina-finan Hausa ba.
Kwanan nan aka yada labarin cewa mawaki Rarara ya mutu. Alhalin yana nan da ransa.
Sadiya ta dade tana fitowa a fina-financial Hausa kafin ta dauke kafa na wani lokaci bayan ta yi aure.

LEAVE A REPLY