Ibrahim Magu

Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, Ibrahim Magu, ta bakin mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, ya yi karin hasken kan batun tsayawa takarar gwamnan jihar Borno da a ke rade-radin Magu zai yi a shekarar zabe ta 2019.

Magu ta bakin Wilson ya karyata wannan batu, inda ya kira wannan rahota da wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta fara fitarwa a matsayin labari maras makama bare tushe.

“Rahoton ba komai bane illa shirin wasu magauta da suka zauna suka shirya zunzurutun karya don su dauke hankalin Magu daga kan ayyukan da ya ke yi na yaki da cin hanci da rashawa da ya samu karbuwa har a kasashen duniya,” inji Wilson.
“Magu ba dan siyasa bane kuma ba shi da niyyar shuga harkar siyasa a yanzu, a saboda haka batun cewa wai yana neman takarar gwamnan jihar Borno zance ne maras tushe.

“Magu ya lura da yadda wasu kafafen yada labarai musamman na yanar gizo suka dukufa wajen bata masa suna da kulla masa sharri iri-iri, wannan dalili ne ma ya sanya ya tuntubi lauyansa don ya tabbata ya nema masa adalci a gaban shari’a bisa labarin kanzon kurege da a ke wallafawa akansa,” inji Wilson.

LEAVE A REPLY