Kungiyar nan ta fafutikar kare ‘yancin Musulmi a Najeriya, MURICta caccaki hukumar shirya jarabawar kammala Sakandire ta yammacin Afurka da aka fi sani da WAEC. A jadawalin fara jarawabar na wannan shekarar hukumar WAEC ta sanya jarabawar ‘Chemistry’ a ranar Juma’a da misalin karfe 2 na rana zuwa karfe 4 na yamma.

A cewar wata sanarwa da MURIC ta fitar ranar Litinin, wannan abinda hukumar ta yi sambai dace ba, domin a daidai lokacin ne Musulmi suke Sallar Juma’a.

A cewar wata sanarwa da MURIC ta fitar ta yi Allah wadai da wannan tsari na yunkurin hana Musulmi zuwa Sallar juma’a, a cewarta daga karfe 1 na rana har zuwa 2:30 al’ummar Musulmi na gudanar da Ibadar Sallar Juma’a.

Sai dai daga bisani, MUSRIC ta samu wani labari da ba ingantacce ba yake cewar hukumar WAEC din sun sauya darasin ‘Chemistry’ a ranar Juma’ar da wasu durussa da suka hada da ‘Ceramic Eassy’ da kuma ‘Forestry Eassy’.

A cewar MURIC wannan anyi ba a yi bane, domin suma darussan guda biyu duk Musulmi suna yinsu, don haka sanya jarabawa a wannan rana a kuma wannan lokaci bai dace ba. Kungiyar MURIC tace neman ilimi wajibi ne ga kowanne Musulmi, dan haka bai dace a hana Musulmi ‘yancin yin addininsa ba.

Haka kuma, kungiyar ta fafutikar kare ‘yancin Musulmi ta MURIC tace sanarwa da aka ce jaridar Premium Times ta fitar ta cewar hukumar WAEC ta sauya jarabawar ‘Chemistry’ da wasu darussa guda biyu baya rubuce a cikin shafin hukumar na intanet, wannan yasa suke zargin labarin ba shi da inganci.

Jaridar ta PT ta ruwaito babban daraktan hulda da jama’ana hukumar shiryar jarabawar ta WAEC dake kula da bangaren Najeriya Mista Demianus Ojijeogu yana mai cewar “Sabida baiwa Musulmi da suke zuwa Sallar juma’a damar yin ibada, jarabawar zata fara ne daga karfe 2:30 na rana ko karfe 3, kafin sannan Musulmi sun idar da Sallar juma’a”

“Wannan sam bai dace ba, domin wannan zance babu wani kwarin guiwa a tare da shi ba zai yuwu ba ace an hana Musulmi zuwa Sallar Juma’a sabida suna son rubuta wannan jarabawar  ta WAEC” A cewar MURIC.

Kungiyar ta MURIC tace ko a shekarar 2015 irin haka ta taba faruwa, inda tace hukumar shirya jarabawar ta sanya karfe 1 zuwa 3 a matsayin lokacin rubuta jarabawa a ranakun juma’a har sau uku.

LEAVE A REPLY