Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta bayyana cewar ta gano gonakin da ake shuka tabar wiwi guda biyar a karamar hukumar Ringin ta jihar Jigawa.

Kakakin hukumar, Asguo Nkereuwem, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a wata sanarwa da ya fitar a birnin Dutse a ranar laraba. Ya bayyana cewar, sakamakon binciken kwakwaf da hukumar ta dukafa da yi a yankin ya sanya ta gano gonakin.

Yayi bayanin cewar, an gano gonakin a kauyuka daban daban a yankin karamar hukumar Ringin.

“Gonakin dai an gano su a kauyen Kagadama da Tsagan da kuma wasu guda uku a yankin Ringin” A cewar kakakin hukumar.

Yace, masu shuka tabar wiwi din sukan yi dabarar cudanya ta da Albasa da Tumatur da kuma sauran kayan lambu domin kada a gane.

Kakakin yace, daya daga cikin mutanan da ake zargi an kama shi tun a ranar26 ga watan Fabrairun da ya gabata a kauyen Kagadama dauke da tabar wiwi da ta kai kilo 12.5 wadda aka yanko ta daga gona.

A cewarsa, daya daga cikin gonakin a kauyen Tsagan, jami’an hukumar sun lalata ta, yayin da ake neman mai gonar ruwa a jallo.

Kakakin rundunar ya cigaba da cewar, guda uku daga cikin gonakin suma an lalata su lokacin da masu gonar suka samu labarin zuwa jami’an hukumar NDLEA zuwa yankin.

Yace wasu daga cikin mutanan yankin da suka taimakawa daya daga cikin masu gonakin arcewa, sun farwa jami’an hukumar ta NDLEA.

Ya cigaba da cewar, ana nan ana cigaba da gudanar da bincike, kuma duk wanda aka kama za’a gurfanar da shi gaban kuliya ba tare da wani jinkiri ba.

LEAVE A REPLY