Hukumar shige-da-fice ta dakatar da jami’anta 2 bisa laifin safarar yara zuwa kasashen Larabawa

Hassan Y.A. Malik

Hukumar shige-da-fice ta kasa ta dakatar da jami’anta 2 bisa samunsu da taimakawa masu safarar mutane.

Jami’an biyu da aka bayyana sunansu da Araoyinbo Oluwadare da Gabriel Awosanmi masu mukamin Senior Inspector of Immigration da kuma Immigration Assistant sun shiga hannun ne a jiya Alhamis a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke jihar Legas.

 

A yau Juma’a kuma bayan wani gajeren bincike da hukumar ta shige-da-ficen ta gudanar, sai ta shelanta dakatar da jami’an biyu ta bakin kakakin hukumar, Mista Sunday James.

Majiyarmu ta bayyana cewa, an samu jami’an biyu da hannu a kitsa safarar yara masu kananan shekaru har su shida zuwa kasashen Oman da Kuwait ta jirgin saman Ethiopian Airlines.

Kwanturola janar na hukumar shige-da-fice, Muhammad Babandede ya umarci dakatar da jami’an da gaggawa don hukumar ta samu damar gudanar da bincike akansu ba tare da wata tangarda ba.

Babandede ya bayyana cewa dakatarwar na cikin kunshin ka’idar aikin hukumar tasu, kuma ya yi alwashin zai yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen fasakaurin mutane zuwa ciki da wajen Nijeriya.

Jami’an tsaron hukumar filayaen jiragen sama na kasa ne suka kama masu laifin a jiya.

LEAVE A REPLY