Hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NAFDAC ta bayyana cewar, jami’anta sun kama kwantena guda 33 makare da kwayar Tramadol wanda aka shigo da su kasarnan, zuwa wani waje da basu sani ba.

Babban daraktan gudanarwa na hukumar NAFDAC, Chritiana Adeyeye ce ta bayyana hakan a Abuja a lokacin da take jawabi gaban wani taron karawa juna sani kan sinadarai.

Haka kuma, hukumar ta bayyana cewar jami’anta sun kama manyan motocin titiri guda uku shake da kwayar ta Tramadol a rukunin masana’antu dake Apapa a jihar Legas.

Taron da ake yi kan samar da tsaro kan sinadarai, ofishin mai baiwa Shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro da hadin guiwar shirin baiwa sinadarai kariya ne suka shirya shirin.

Daraktar Hukumar ta NAFDAC ta bayyana cewa, dole ne a kafa dokar ta baci akan kwayoyi a kasarnan, akan matasa da yara kanana.

Madam Adeyeye  tace “Dole ne mu kafa dokar ta baci a sashin kwayoyi a kasarnan, idan ba haka ba muga abinda ba daidai ba”

“A yanzu haka da nake yi muku magana, akwai akalla kwantena 33 ta kwayar Tramadol da hukumarmu ta kama. Wadannan fa wadan da muka iya gani ne kawai muke kamawa, inda wanda ake shigewa da su a boye”

“Muna da gagarumar matsala a kasarnan, ya zama tilas a kafa dokar ta baci a sashin kwayoyi na kasarnan, sabida yaranmu da matasanmu sune suke sha suke lalacewa”

“Kamar mako biyar da suka wuce, hukumar NAFDAC ta kama kwantena mai kafa 40 cike da kwayar Tramadol da kuma wasu motoci makare da kwayar a Apapa a jihar legas. An gaya mana cewarkwayar za’a kaita Yola ne, wanda babu mamaki ace a wuce da ita Sambisa daga nan”

“Tayaya za’a ce mace budurwa ta daura bom a jikinta ya tashi da ita, idan babu aikin kwaya” Muna da gagarumar matsala a gabanmu”

 

LEAVE A REPLY