Hukumar lafiya ta duniya da aka fi sani da WHO, tare da hadin guiwar wasu kungiyoyi masu zaman kansu, a ranar litinin, suka gabatar da tallafin keken hawa guda 853 ga Gwamnatin tarayyar Najeriya, domin rabawa jami’an lafiya.

Babban daraktan WHO na Najeriya, Wondi Alemu, shi ne ya mika kyautar kekunan ga ministan lafiya na kasa Isaac Adewole a birnin tarayya Abuja, yace sun baiwa Najeriya tallain kekunan ne domin rabawa jami’an lafiya.

A cewarsa, jm’an lafiyar zasu yi amfani da kekuna domin wayar da kan mutane, tare da kai rahoton barkewar cututtuka cikin sauri, wanda hakar zai taimaka wajen dakile yaduwar cututtuka cikin sauri.

“Bayar da bayanai kan bullar cututtuka zai taimaka matuka wajen dakile yaduwarta, kuma zai sanya a dauki matakan gaggawa kan duk wata barazana”

“Wannan tallafin kekuna, mun tabbatar zai taimakawa gwamnati da al’ummar Najeriya matuka, wajen yin rigakafin barkewar cututtuka”

Sannan Mista Alemu ya bukaci Ministan lafiyar da ya tabbatar anyi amfani da kekunan ta hanyar da ta dace, an kuma danka su a hannun wadan da zasu yi amfani da su.

A lokacin da yake nasa jawabin, Ministan lafiya na Najeriya, ya yabawa kokarin WHO akan wannan aikin alheri da suka yi na taimakawa da wadannan kekuna domin dakile yaduwar cututtuka.

“Zamu yi duk abinda ya dace, na dakile yaduwar cututtukan da ake saurin kamuwa da su a duk lokacin da wata annoba ta taso, ta hanyar yin amfani da wadannan kekuna”

“Wadannan kekuna da aka bayar za a danka su a hannun DSNO ne a lokacin da ya dace”

“Za kuma a alkintasu, tare da tabbatar da ganin cewar an yi amfani da su ta hanyar da ta dace”

 

NAN

LEAVE A REPLY