Dakarun Hukumar kwastan ta kasa dake aiki kan iyakar Seme a Badagiri ta bayyana cewar ta lalata jabun magungunan Kodin da ta kama na miliyoyin kudade, wadan da an biya musu harajin sama da Naira miliyan 102.4.

Kakakin rundunar, Saidu Abdullahi shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Legas a ranar Larabarnan.

Ya kara da cewar, an yi bikin lalata jabun magungunan ne a kan idon jami’an hukumar kula da ingancin kayayyaki ta Najeriya NAFDAC, da kuma babban jami’in hukumar Mojisola Adeyeye da jami’an hukumar kwastan karkashin Mohammed ALiyu.

Magungunan da aka kama aka lalata su sun hada da: Turamadol na ruwa da na kwaya; da Kodin da Dizafam da Analjin da Medik 5 da Farasitamol mai dauke da kafen da sauran dangoginsu.

Sauran kayayyakin da hukumar ta lalata sun hada da Shinkafa da takin zamani da kayan abinci na cikin gwangwani.

 

LEAVE A REPLY