Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Jami’an hukumar hana fasa kwauri ta kasa kwastam sun kai wani samame gidan gwamnan jihar sokkoto, Aminu Waziri Tambuwal sannan sukai awon gaba da motoci kusan 160 da hukumar ke zargin gwamnan ya shigo dasu ba bias ka’ida ba.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa jami’an sun kai samamen ne a daren jiya Laraba kuma nan gaba kadan hukumar zata kira taron manema labarai domin sanar da duniya halin da ake ciki da kuma matakin da hukumar ta dauka.

Ana zargin dai gwamnan ya siyo motocinnne domin yin amfani dasu a zaben shekara ta 2019 mai zuwa bayan da ake tunanin gwamnan zai sake tsayawa takara a karo na biyu inda tuni alamu suka fara bayyana hakan.

Sai dai kawo yanzu gwamnatin jihar batace komai ba akan lamarin yayinda al’umar jihar suke ta tofa albarkacin bakinsu akan lamarin.

Hukumar kwastam dai karkashin jagorancin Kanal Hamidu Ali Mai ritaya taci alwashin dakile duk wani yunkuri na da shigo da motoci ba bias ka’ida ba.

LEAVE A REPLY