Danjuma Goje
Daga Babale Gombe
Hukumar nan mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya , wato EFCC, zata sake gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Gombe Alh. Danjuma Goje a gaban kotu a ranar 10 ga afrilun wannan shekara da muke ciki saboda yin zambar kudi har naira biliyan 5. EFCC za ta sake gurfanar da Danjuma Gojen ne tare da wassu mutane 3 da suka had’a da Alh. Aliyu El-Nafaty, S.M. Dokoro da kuma Alh. Sabo Tumu kuma zasu gurfana ne a babban kotun gwamnatin tarayya dake garin Gombe. Sake gurfanarwan ya biyo bayan wassu gyara-gyare ne da EFCCn ta yiwa tuhume-tuhumen da akeyi musu.
Shi dai Danjuma Goje ana tuhumar sa ne da karb’an bashi daga bankin Access har na naira biliyan 5 bayan yayi sojan gona ta hanyar sanya hannu na bogi akan takardun da suka taimaka masa karb’an bashin kudaden don yin aiyukan raya kasa amma ya karkatar da su Ta hanya daban. Tuhumar da ake yiwa Sabo Tumu na da alaka ne da kwangilar samar da abinci a gidan gwamnatin jihar Gombe. Haka kuma EFCC na tuhumar S.M. Dokoro ne da taimakawa wajen rarraba wassu motoci har guda 50 kirar Toyota Hiace mallakar jihar Gombe ga wassu mutane akan kudi naira miliyan 22 alhalin kiyasin kudaden motocin ya kai kimanin naira miliyan 250. Shi kuma El-Nafaty a nasa bangaren EFCC na tuhumar sa ne da had’a baki da Danjuma Goje wajen karkatar da naira biliyan 1 da miliyan 600 daga hukumar ilimin bai d’aya na jihar Gombe wato SUBEB.
Ashe naira biliyan 1 da miliyan 600 ba su kai a rushe Government Comprehensible Day Secondary School dake Gombe a sake gina sabuwa ba?

LEAVE A REPLY