Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero

Hukumar dake yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta kama tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero kan batun kudin zabe Naira miliyan 700 da ya karba.

Ramalan Yero dai ya shafe kusan sa’o’i 4 a ofishin hukumar dake jihar kaduna yana amsa tambayoyi a ranar Juma’a, inda kuma daga bisani aka sallame shi da misalin karfe 1:30 na rana, yana mai yin murmushi.

Tsohon Gwamnan ya godewa magoya bayansa wadan da suka yi tururuwa zuwa harabar ofishin hukumar domin jajanta masa, da ya fito yaga dandazon magoya bayansa, inda yayi musu godiya kan yaddasuka tsaya da shi a tsawon lokacin da ya shafe a harabar ofishin hukumar.

LEAVE A REPLY