Dr. Isah Ali Pantami Shugaban hukumar NITDA

Daga Hassan Y.A. Malik

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa, NITDA ta horas da mata 111 yin amfani da fasahar sadarwa ta zamani a jihar Jigawa.

Babban Daraktan Hukumar, Dr Isa Pantami ne ya sanar da hakan a wajen bikin rufe bada horon a Dutse, babban birnin na jihar Jigawa.

Pantami y ace, an zabo matan ne daga jihohi bakwai na shiyyar arewa maso yammacin kasar nan.

Ya ce bada horon na daga ckin kudirin hukumar na horas da mata hanyoyin yin amfani da fasahar sadarwa na zamani a yankin arewa maso yammacn kasar nan.

Pantami ya bayyana fasahar sadarwa ta zamani a matsayin sabon abin da ake ya yi tare da cewar bada horon zai kuma samar da ayyukan yi da kuma mayar da matan jihohin bakwai masu dogaro da kai.

Ya kara da cewa dukkannin matan da aka baiwa horon su 111 sun sami komputa ta tafi da gidanka.

LEAVE A REPLY