Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kaduna a ranar Alhamis ta bayyana cewar ta sanya ranar Juma’a 29 ga watannan na Yuni a matsayin rana ta karshe domin kammala biyan kudin aikin Hajjin bana a jihar.

Kakakin hukumar jindadin Alhazan jihar, Yunusa Abdullahi, shi ne ya bayyana manema labarai hakan a Kaduna, yace sanya ranar ya zama dole ne domin cika umar hukumar aikin hajji ta kasa da ta sanya ranar 30 ga watan Yuni domin dukkan jihohi su kammala biyan kudin aikin hajjin bana.

Ya gargadi mahajattan bana daga jihar da suka yi nufin sauke farali, da su hanzarta kammala biyan kudinsu, in ba haka ba zasu rasa damarsu ta zuwa aikin hajjin bana.

“Kudin da aka amince da su kowanne mahajjaci a jihar zai biya shi ne Naira miliyan daya da dubu dari hudu da casa’in da dari shida da gima sha hudu da digo biya (N1,490,614.05) wato an samu raguwar Naira 44,889.95 akan abinda aka biya shekarar 2017”

NAN

LEAVE A REPLY