Gwamnan jihar Filatu, Simon Lalong

Daga Hassan Y.A. Malik

Kididdiga ya nuna cewa, a tsakanin Juma’ar da ta gabata zuwa Asabar, akalla mutane 23 da suka mutu a sakamakon harin da Fulani makiyaya suka kai a kan garin Josho da ke yankin Daffo cikin karamar hukumar Bokkos, a jihar filato ne aka binne, inda wasu da dama suka jikkata haka kuma akalla mutane 2,000 suka rasa matsugunansu.
Wata majiyar ta bayyana cewa, a ranar Juma’a kadai an samu gawarwaki mutane 18 kuma an binne su a wannan rana, haka kuma an sake binne wasu gawarwakin da aka samu a ranar Asabar, sai dai adadin bai kai na ranar Juma’a ba.

Shugaban karamar hukumar ta Bokkos, Simon Angyol, ya bayyanawa manema labarai a jiya cewa mutane 16 ne aka tabbatar da mutuwarsu kuma tuni aka binnesu.

Sai dai wani malamin addini a garin na Daffo ya bayyana cewa adadin da shugaban karamar hukumar tasu ya bayar ya rage adadin mutanen da harin ya salwantar domin kwa sun fi 16 da ya fadawa manema labarai.

Malamin ya ci gaba da cewa fulanin sun farmaki kauyuka biyar ne, da suka hada da: Nghakudung, Morok, Hottom, Wareng da Ganda.
Har yanzu dai ana ci gaba da neman mutanen da zuwa yanzu ba a ji duriyarsu ba don tabbatar da adadin mutanen da suka rasa rayukansu a harin na daren Alhamis.

Wannan lamari da ya yi matukar harzuka gwamnatin jihar Filato ya sanya ta yi alwashin zakulo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki atre da tabbatar musu da hukuncin da ya dace da su.

Gwamnan jihar Filato, Solomon Lalong ta bakin kwamishinan yada labaran jihar, Yakubu Dati, ya jajantawa al’ummar karamar hukumar Bokkos tare da tabbatar musu da cewa wadanda suka aikata wannan mummunan laifi ba za su tsira daga doka ba, domin dai duk wanda ba ya martaba ran dan adam, to, babban mai laifi ne.
Gwamnan ya koka kan yadda jihar Filato ba ta cikakken ikon bawa al’ummarta tsaron da ya kamata, tare da yin alkawarin baiwa jami’an tsaron gwamnatin tarayya goyon baya da duk wani agaji da suke bukata don tsare dukiya da rayukan al’ummar jihar Filato.

“Za mu kaddamar da motoci kirar Hilux guda 40 da muka saya don karafafawa jami’an tsaro. Sufeta janr na ‘yan sandan Nijeriya ne zai kaddamar da su nan ba dadewa ba.”

Kwamishinan ya roki al’umma da su yi gaggawar sanar da jami’an tsaro duk wani motsi da ba su aminta da shi ba, don daukar matakin da zai hana afkuwar rasa rayuka da dukiyoyin al’umma.

LEAVE A REPLY