Opeyemi Bamidele

Wani dan bindiga da ba’a san ko waye ba, ya harbi tsohon dan majalisar tarayyar Najeriya, Opayemi Bamidelejigo a cikin jam’iyyar APC a jihar Ekiti a yayin wani gangamin siyasa da dan takarar Gwamnan jihar John Kayode Fayemi ya shirya a sakatariyar jam’iyyar APC a Ado Ekiti.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar taron wanda ya hada dubban magoya bayan Fayemi a harabar Sakatariyar jam’iyyar APC a Ado Ekiti, ya samu halartar Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu da tsohon Minista Dayo Adeyeye da sauran jiga jigan jam’iyyar a shiyyar kudu maso yamma.

Wani mutum ne da ba’a san ko waye ba ya harbi tsohon dan majalisar a hannu a wajen taron, inda daga bisani kuma ‘yan sanda suka yi harbi a sama, domin tarwatsa gungun jama’ar da suka taru a wajen domin bayar da dama a fice da manyan mutanan da suke wajen taron.

Tuni dai aka garzaya da dan majalisar zuwa wani asibiti dake kusa domin bashi kulawar gaggawa kan harbin da aka yi masa a hannu, sai dai kuma, an harbi wani mutum da ba’a tantance ko waye ba a wajen wannan taron gangamin siyasar.

LEAVE A REPLY