Shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawa Sanata mai wakiltar kudancin jihar Borno a majalisar dattijai ta kasa, Abubakar Kyari, ya kalubalanci Ministan tsaron Najeriya Mansur Dan-Ali da yace an kawo karshen Boko haram a Najeriya.

Ministan tsaron ya bayyana cewar an kawo karshen ayyukan ta’addanci na ‘yan kungiyar Boko Haram ne a wani taron jin ra’ayin jama’a da aka gudanar tsakanin al’umma da jami’an tsaro a birnin Maiduguri.

Minisstan yace, dukkan kananan hukumomi 12 da Boko Haram suka karbe ikonsu a baya, yanzu duk sojoji sun dawo da su hannun Gwamnatin Najeriya.

Yana bayyana hakan ne, a lokacin da yake zayyano irin nasarorin da soja suka samu a wannan yaki da suke yi da ‘yan kungiyar Boko Haram.

“Bari na tabbatar muku cewar, a halin da ake ciki a yanzu, babu wani yanki na Najeriya da yake karkashin ‘yan kungiyar Boko Haram”

“Misali, kafin zuwan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, kananan hukumomi 12 a cikin 27 dake jihar Borno suna karkashin kulawar kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram. Amma a yau duk an kwato su”

“Haka kuma, a wannan lokacin da aka sace kusan mutane 30,000 kusan duk an samu an kubutar da su. A sakamakon wasu sauye sauye da aka samu a rundunar Lafiya Dole a kwanakin nan, ya sanya aka rubanya kokarin da ake yi, wannan ne kuma ya sa aka samu nasarar fafarar ‘yan ta’adda a dajin Sambisa”

“Haka kuma, mun sake rubanya kokari, wajen kula da walwalar sojojin dake fagen daga, muna biyansu dukkan hakkokinsu akan kari, bugu da kari, muna samar musu da duk abinda suka bukata na makamai da sauran kayan yaki akan lokaci”

“Ma’aikatar tsaro ta Najeriya, ta baiwa sojoji da dama horo na musamman akan sabbin dabarun yaki da ‘yan ta’adda” A cewar Ministan tsaro.

A lokacin da yake mayar da martani kan wannan kalamai na Ministan, Sanata Abaubakar Kyari, yace har yanzu karamar hukumar Marte tana karkashin kulawar Boko Haram, kuma sojojin Najeriya sun kasa karbota daga hannun ‘yan ta’adda.

A cewarsa, babu ko tantama Sojojin Najeriya sun yi kokari wajen darkake ayyukan ‘yan kungiyar Boko Haram a gurare da dama, amma dai duk da haka ana bukatar karin kuzarin aiki wajen kwato karamar hukumar Marte.

Sanata Kyari yace, har yanzu harkoki basu koma yadda suke ba a garuruwan da sojin suke cewar sun kwato daga hannun’yan Boko Haram din.

Daga nan, ya bukaci rundunar sojojin Najeriya ta rubanya kokari wajen ganin an kwato dukkan wani waje da yake karkashin ikon ‘yan kungiyar Boko Haram a jihar da ma sauran Najeriya.

LEAVE A REPLY