Yusuf Buhari

Fadar Shugaban kasa ta fitar da wata sanarwa da take karyata wani rahoto da yake nuna cewar an fitar da Yusuf Buhari zuwa kasar Jamus domin cigaba da jinyarsa a can da bashi kulawa ta musamman, sanarwar  tace wannan rahoto babu kanshin gaskiya acikinsa.

Mai Magana da yawun Shugaban kasa akan kafafen yada labarai, Garba Shehu ya shaidawa DAILY NIGERIAN ta wayar tarho ‘yan mintoci kada da suka gabata, inda yake karyata jita jitar cewar an fitar da Yusuf Buhari zuwa kasar waje, yace har yanzu Yusuf Buhari yana karbar magani a Najeriya.

Da wakilin DAILY NIGERIAN ya tambayi Garba Shehu kan halin da Yusuf Buhari yake ciki, yace shima ba shi da masaniya domin bai ziyarci asibitin ba a ranar Alhamis.

Idan ba’a manta ba DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar ana sa ran an fitar da Yusuf Buhari zuwa kasar waje a jirgin daukar marasa lafiya.

Yusuf Buhari dai yaji wani mummunan ciwo ne tare da buguwa akansa yain da yayi taho mu gama a wani mummunan hadarin babur da yayi shi da abokinsa a lokacin da suke wasan tsere a unguwar Gwarinfa a birnin tarayya Abuja.

Wata majiya t ace,halin da Yusuf yake cikin a yanzu ya tsananta, amma dai likitoci sunce ana kokarin shawo kan halin da yake ciki.

 

 

 

LEAVE A REPLY