Hakeem Baba-Ahmed

Shugaban ma’aikatan shugaban majalisar dattawa na kasa Bukola Saraki, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Hakeem ya bayyana cewar wannan sauya sheka da yayi bata shafi Shugaban majalisardattawa ba.

Ya bayyana cewar doole ta sanya ya dauki wannan matakin na ficewa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP mai adawa. Yace bai yanke wannan hukunci ba sai da ya shawarci ‘yan bangaren APC Akida na jihar Kaduna.

Bangaren jam’iyyar APC Akida a jihar Kaduna na tare da Sanata Shehu Sani wanda shima ya nuna alamun tsallakewa daga jam’iyyar ta APC daga yanzu zuwa ko wane lokaci.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a jihar Kaduna, Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewar sai da ya aikewa uwar jam’iyyar ta APC a jihar wasikar ficewarsa daga cikin jam’iyyar.

 

 

LEAVE A REPLY