Galibin Alhazan Najeriya dake Kasa mai tsarki sun bazama kasuwanni domin yin sayayya yayin da suka kammala ibadar aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.

Akalla Alhazan Najeriya 50,000 je yanzu haka suke kasar Saudiyya bayan da suka kammala rukuni na biyar a cikin addinin Musulunci. Shugaban hukumar kula da aikin Hajji ta Kasa Abdullahi Mukhtar ya tabbatar da adadin Alhazan dake Kasa mai tsarki.

Wakilin DailyNigerian dake Kasa mai tsarki, ya bayyana mana cewar bayan kammala Sallar Juma’a a jiya ne dai Alhazan suka fantsama a cikin kasuwanni suna saye saye domin yin tsaraba yayin da zasu fara haramar dawowa gida.

LEAVE A REPLY