Mutumin da ya lashe zaben Sanata a kasar Italiya

Wani haifaffen birnin Gusau da ke jihar Zamfara a Najeriya amma mazaunin Italiya ya yi nasarar lashe kujerar sanata a Majalisar Dattawan kasar, in da ya zama mutun na farko bakar fata da aka zaba akan wannan mukami a duk fadin kasar.

Toni Iwobi ya lashe zaben ne a karkashin jami’yyar League Party mai adawa da kwararar baki a mazabar Brescia da ke arewacin Italiya.

An haifi Iwobi a garin Gusau dake jihar Zamfara amma tun a shekara ta 1970 ya ke zaune a Italiya.

Iwobi ya shafe sama da shekaru 20 a matsayin mai goyon bayan jam’iyyar League Party , in da ya shiga sahun masu yaki da kwararar bakin haure daga nahiyar Afrika.

Sabon Sanatan ya ce, kwararar bakin haure cikin Italiya ba bisa ka’ida ba na tsananta matslar wariyar launin fata a kasar.

Mr. Iwobi ya shiga Italiya a matsayin dalibi shekaru 40 da suka gabata, in da ya auri baturiyar kasar kafin daga bisani ya bude kamfanin fasahar sadarwa.

 

Madogara

www.m.ha.fri.fr

LEAVE A REPLY