Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Daga Hassan Y.A. Malik

Mai bawa gwamnan jihar Kano shawara na musamman akan harkokin sabbin kafafen yade labarai, Salihu Tanko Yakasai ya fadawa jaridar Vanguard a jiya cewa sakarci ne ya bar ofishinsa ga Darakta janar na yada labarai, Aminu Yassar wanda ya ke kasa da shi.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnan, Dakta Abdulahi Umar Ganduje ya karawa Yakasai girma daga mukamin darakta janar zuwa na mai bada shawara na musamman, yayin da aka maye gurbinsa da babban sakataren yada labarai na gwamnatin, Yassar.

Tun bayan da aka kara masu girma ne Yassar da tsohon maigidansa, Yakasai, ke hargitsi game da wanda zai rike ofishin darakta janar.

A cewar Yakasai, a tsarin mukaman gwamnati, mukamin hadimi shi ne mafi girma domin kuwa daidai ya ke da na kwamishina, yayin da darakta janar ya ke daidai da babban sakatare.

Ya ce “Gwamnati za ta iya baiwa kowane jami’i ofishin da ta ga dama, kuma ni wannan ofishi aka ba ni. Ba da karfi na kwata ba”

Ya ci gaba da cewa “Ba gidan ubana ba ne. A yau idan aka ce na bar ofishin, kafin ku ce Vanguard, na fita daga nan.”

Yakasai ya kara da cewa tun da ya fara aiki a gwamnatin Ganduje shekaru 2 da suka gabata, ya yi kokarin mutunta wadanda suke aiki tare kuma za su ci gaba wayar da kan jama’a game da ayyukan gwamnatin.

LEAVE A REPLY