Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam

Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, ya kaddamar da sayar  da takin zamani mafi arha a najeriya, domin kuwa gwamnatin na sayar da takin NPK akan kudi Naira dubu uku kacal akan kowace jaka a dukkan fadin jihar.

Bincike dai ya nuna cewar a Kasuwa ana sayar da takin zamani na NPK akan kudi Naira 8,500.Yayin da Gwamnan ya zaftare farashinsa da kashi 65 da ake sayarwa da manoma, kuma wannan shi ne farashi mafi kankanta da ake sayar da takin zamani a Najeriya.

Gwamnan ya kaddamar da fara sayarda takin ne a ranar Litinin a babban birnin jihar Damaturu, inda ya bayyana cewar Gwamnatinsa ta tanadi takin zamani na NPK da yawansa ya kai Tan 8,460.

Gwamnan ya ce Gwamnatinsa ta kashe zunzurutun kudi Naira Biliyan 1,468,800, 000.00 domin sayo takin tare da rarraba shi a daukacin kananan hukumomin jihar 17 domin sayarwa a farashi mai sauki.

 

 

LEAVE A REPLY