Gwamnatin tarayya ta ware zunzurutun kudi Naira miliyan 186 domin sayan galla gallan motoci na alfarma ga tsaffin Shugabannin kasarnan da mataimakansu.

Wadan da zasu ci gajiyar wadannan motocin sune: Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo, Olushegun Obasanjo da tsohon mataimakinsa Atiku ABubakar.

Sauran sune tsohon Shugaban Ibrahim Badamasi Babangida da Yakubu Gowon da Abdulsalami Abubakar da Shagari da kuma Shonekan.

Wannan daya daga abinda Gwamnati ta rubuta a cikin kasafin kudi na shekarar 2018, wanda aka gabatarwa da Shugaban kwamatin kula da kasafin daga ofishin Sakataren Gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Gida Mustapha.

A cikin kudin,an ware Naira Miliyan 96 ga tsaffin Shugabannin kasarnan, da kuma Naira Miliyan 90 ga tsaffin mataimakan Shugabannin kasa.

DAILY TRUST

LEAVE A REPLY