Shugaba Muhammadu Buhari

Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da fitar da Naira biliayn 10 don gyara kauyikan da fulani makiyaya suka lalata a jiahr Binuwai da sauran sassan kasar nan.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa wajen kawo karshen kashe-kashen da fulani makiyayan ke yi ga ‘yan Nijeriya da basu ji ba basu gani ba.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya fidda wannan sanarwa a jiya Talata a ziyarar da ya kai jihar Binuwai.

Osinbajo ya yabawa gwamnan jihar ta Binwai, Samuel Ortom bisa jajircewarsa wajen ganin ya tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jiharsa duk kuwa da kalubalen tsaro da ya ke da shi a jihar.

Ya ce, “Shugaba Buhari ya amince da fitar da Naira biliyan 10 don sake gina kauyuka da gonakin da fulani makiyaya suka lalata a jihar Binwai da ma sauran wurare da suka fuskanci wannan matsala a fadin kasar nan.

“Shugaba Buhari ya umarci ni da na baiwa wannan lamari muhimmanci a saboda haka za ku ke gani na a kai-a kai. Gwamnatin Nijeriya ta dukufa wajen ganin ta kare rayukanku da dukiyoyinku.”

LEAVE A REPLY