Ana sa ran akalla daliban firame 400,000 ne zasu ci gajiyar shirin Gwamnatin tarayya na ciyarwa a makarantun Gwamnati a jihar Adamawa, a cewar sanarwa daga hukumomi.

Babban darakta a hukumar wayar da kan al’umma ta kasa NOA, Ahmad Abba shi ne ya bayar da wannan sanarwa ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, a birnin Yola a ranar Talata.

Abba yace daliban da zasu ci gajiyar wannan ciyarwa a makarantun gwamnati su ne daliban aji daya zuwa aji uku, daga bisani kuma Gwamnatin jihar zata dauki dawainiyar dalibai ‘yan aji hudu zuwa aji shida.

“Gwamnatin tarayya ta ware ranar 1 ga watan Afrilu domin fara wannan shiri a jihar Adamawa”

“Akalla yara 400,000 ne ake sa ran zasu amfana da wannan ciyarwa a makarantun firame na Gwamnati a jihar ta Adamawa” A cewarAbba.

Ya kara da cewar, lokacin da aka sanya hannun yarjejeniyar amincewa da wannan shiri tsakanin Gwamnatin tarayya da ta jihar Adamawa, an bayyana cewar, gwamnatin Adamawa zata dauki nauyin ciyar da daliban aji hudu zuwa aji shida.

A cewar Abba, wannan shirin an tsara shi ne domin ciyar da ‘ya ‘yan talakawa wadan da ba sa iya samun abinci sau uku a gidajensu.

“Da aka bayar da rahoton fara ciyarwar a jihar Adamawa, dalibai sun cika makarantun Gwamnati dake jihar”

NAN

LEAVE A REPLY